Connect with us

Labarai

An ɗage ranar komawa karatu a jami’o’in Nijar

Published

on

Ma’aikatar ilimi mai zurfi ta jamhuriyyar Nijar ta ɗage ranar komawa karatu a jami’o’in ƙasa daga 1 ga watan Satumba mai kamawa zuwa 13 ga watan.

Rahotanni sun ce, ƙungiyar malaman jami’o’in ƙasar ce ta nemi Gwamnati ta ƙara wa’adin hutun, domin malamai su ƙara kimtsawa.

Freedom Radio ta tuntuɓi sakataren ƙungiyar malaman jami’o’i reshen jihar Tahoua Malam Namaiwa Atto Muhammadu ya ce, malamai basu gama shirin komawa ba, saboda sun yi ayyuka da yawa kafin hutu.

Namaiwa ya ce, Malaman sun yi aikin jarrabawar neman ƙwarewa ɗalibai da aka yi a makon da ya gabata, alhali suna cikin hutu, don haka suka nemi ƙari domin cike gurbin lokacinsu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!