Labarai
An Ƙaddamar da majalisar gudanarwar Kotun sulhu ta Kano

Hukumar shari’a ta jihar Kano, ta ƙaddamar da majalisar gudanarwar Kotun sulhu da nufin kawo ƙarshen matsalolin da ake fuskanta musamman ma na yawan shari’u a kotunan.
Babbar join jiha Mai shari’a Dije Abdu Aboki ce ta ƙaddamar da majalisar a yau Litinin, inda ta bayyana hakan a matsayin babban ci gaba a fannin shari’a.
Haka kuma ta ja hankalin mambobin majalisar da su gudanar da aikinsu yadda ya kamata.
Malam Yahaya Muhammad Sani, shi ne Muƙaddashin Daraktan Kotun Sulhun, ya bayyana cewa za a riƙa mayar da hukuncin da kotun Sulhun ta yi a matsayin hukuncin babbar kotun jihar Kano.
Ya ce, “Ita wannan kotun tana yin sulhu da sasanci ne a kan abubuwan da suka shafi rikici tsakanin makwafta da saɓani a tsakanin iyali warware matsalar bashi”.
“Maimakon mutum ya kai ƙara kotu kai tsaye ko kuma ofishin ƴan sanda, idan ya kawo ƙara za a saurareta ne a nan a kuma yi hukuncin da ya dace ba tare da zalintar kowa ba.”
Mambobin majalisar gudanarwar Kotun sulhun sun haɗa:
1. Hon. Grand Kadi Shari’a Court of Appeal, Kano State – Mamba.
2. Hon. Attorney General/Commissioner for Justice, Kano State – Babban Lauya (AG) kuma Kwamishinan Shari’a na Jihar Kano.
3. Hon. Justice Ibrahim Musa Karaye (Hon. ADR Judge) – Alƙali mai zaman kansa kan harkokin sasanci da sulhu (ADR).
4. Upper Sharia Court Judge (to be appointed by the Hon. Chief Judge) – Alƙalin Babbar Kotun Shari’a da Babban Alƙali zai naɗa.
5. H. H. Suleiman Esq. (Chief Registrar, High Court of Justice, Kano State) – Babban Rajistar Babbar Kotun Jihar Kano.
6. Abubakar Haruna Khalil Esq. (Chief Registrar, Sharia Court of Appeal, Kano State) – Babban Rajistar Kotun Shari’a ta Ƙoli, Kano.
7. Barr. Sagir Gezawa – Wakili daga kungiyar NBA reshen Kano.
8. Barr. Bashir Isa – Wakili daga NBA reshen Ungogo.
9. Abdullahi Adamu – Wakili daga Hukumar Shari’a (Sharia Commission).
10. Alhaji Bello Habibu Dankadai – Wakili daga Majalisar Masarautar Kano.
11. Yahaya Muhammad Sani – Mukaddashin Darakta na KMDC.
12. Tsohuwar Shugabar FIDA – Wacce ta jagoranci ƙungiyar lauyoyin mata ta duniya (Federation of International Women Lawyers).
13. Malam Ibrahim Khalil – Wakili daga Majalisar Malamai ta Najeriya, reshen Kano.
You must be logged in to post a comment Login