Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An bankaɗo maɓoyar masu garkuwa da mutane a Kano

Published

on

Ƴan sanda sun bankaɗo maɓoyar masu garkuwa da mutane a unguwar Jaba da ke nan Kano.

Wani shaidar gani da ido ya ce, ƴan sandan sun biyo sahun masu garkuwar ne a wani gidan haya da suka kama.

An samu bindigu ƙirar AK47 da kuma cafke mutum huɗu maza da mace ɗaya a gidan, a cewar shaidar.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƴan sandan Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sai dai bai yi ƙarin bayani ba, inda ya ce suna ci gaba da bincike kan lamarin a halin yanzu.

Karin labarai:

Yadda mutane 3 suka rasa rayukan su sanadiyar tashin gobara a Kano

Kano: Ƴan bindiga sun kai hari garin Minjibir

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!