Labarai
An bankaɗo badaƙalar kuɗi ta sama da biliyan goma- HALCIA
Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta jamhuriyyar Nijar wato HALCIA ta bankaɗo wasu baɗaƙalar kuɗi, na sama da biliyan goma na Cfa.
Hakan ya fito ne a wani rohoto da ta fitar a ƙarshen makon nan da ya gabata.
Sai dai wasu ƙungiyoyin farar hula sun bayyana takaicin su game da yadda ba’a hukunta wadanda aka kama da laifi, kamar yadda Sule Umaru shugaban wata ƙungiyar farar hula a ƙasae ya bayyanawa Freedom Radio cewa “ ya kamata ace hukumar yaƙi da rashawar ta fito tayiwa al’umma bayani tare da hukunta wadanda aka samu da badaƙalar”
Sai kuma Shugaban hukamar ta HALCIA Salisu Uban doma ya bayyana cewa su aikin su shine binciko masu laifi kawai sauran hukunci kuma ya rage wa kotu.
You must be logged in to post a comment Login