Labarai
An binne ’yan kasuwar Jos da aka kashe a Barkin Ladi

An gano gawarwakin ’yan kasuwar da aka kai wa hari aka kashe a hanyarsu ta zuwa ƙaramar hukumar Pankshin daga Jos, inda aka birne su a ƙaramar hukumar Barkin Ladi ta jihar Plateau.
Rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa ya ce mamatan, waɗanda ’yan uwansu suka bayyana cewa suna zuwa Pankshin duk mako domin kasuwancin takalma, an yi musu jana’iza ne a yammacin ranar Litinin a makabartar Sabon Anguwa da ke garin Barkin Ladi.
Majiyoyin gwamnati sun shaida wa jaridar cewa an zaɓi a binne su ne a wajen al’ummominsu domin kauce wa tashin hankali da ka iya ɓarkewa sakamakon kisan. Mamatan dai mazauna unguwar Yandoya ne a ƙaramar hukumar Jos North.
Wani jagoran matasa a Barkin Ladi, Danjuma Ibrahim, ya tabbatar da binne su, yana mai cewa an sanar da su tun da rana cewa za a kawo gawarwakin domin yi musu jana’iza a can, domin kwantar da tarzoma a Jos.
Ya ƙara da cewa su shida ne suka fuskanci harin, amma biyu sun tsira, yayin da aka binne huɗu. Ya kuma yi kira ga al’umma da su kwantar da hankalinsu, su kasance masu bin doka, tare da roƙon gwamnati da hukumomin tsaro su ɗauki matakan kawo ƙarshen tashin hankalin da ke ƙara yawaita a yankunan da abin ya shafa.
You must be logged in to post a comment Login