Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An buɗe harkokin sadarwa a Gusau babban birnin jihar Zamfara

Published

on

Gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa ta dawo da harkokin sadarwa a Gusau babban birnin jihar a ranar Juma’a 1 ga watan Oktoba.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Zailani Baffa ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio ta wayar tarho.

Zailani Baffa ya ƙara da cewa, ya zuwa yanzu akwai matsalar Network da ake fuskanta a babban birnin.

Sai dai ya bada tabbacin cewa nan ba da daɗewa ba za a magance matsalar.

“Duk da cewa sai a hankali komai zai zama dai dai sakamakon yadda aka cire network din tsawon lokaci, a yanzu ba kowa ne zai iya samun yadda yake so ba kamar baya” in ji Zailani Baffa.

Baffa ya tabbar da cewa an dawo da harkokin sadarwar ne biyo bayan kyakkyawan rahoton da gwamnati ta samu na nasarar yaƙar ƴan ta’adda a Gusau.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!