Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Coronavirus

An bude cibiyar killace masu korona da ke Sani Abacha

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta ce duk da alkaluma sun nuna cewa Jihar Kano na kan gaba wajen samun nasarar yakar cutar Corona, to amma wajibi ne a ci gaba da daukar matakan kariya daga cutar.

Gwamna Dr Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake karbar bakuncin jami’an cibiyar killace masu cutar dake filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata, wadda Alhaji Aliko Dangote ya samar.

Ya kara da cewa a yanzu haka kididdiga ta nuna cewa Kano ce ta 11 a masu kamuwa da cutar a kasar nan, wanda ke nuna gagarumar nasara in aka samu, la’akari da yadda a baya ita ce ta uku, a don haka ne ya godewa Alhaji Aliko Dangote bisa samar da cibiyar wacce aka kammala ta.

A na sa bangaren Alhaji Abdulkadir Sidi wanda ya wakilci Alhaji Aliko Dangote, ya ce an kirkiri cibiyar ne don taimakon gwamnati wajen yaki da cutar Corona, inda aka sanya na’urori da dama da kudinsu ya kai kimanin naira miliyan 500, sannan tana dauke da gadaje 200, dari a bangaren mata dari a bangaren maza.

Wakiliyarmu Zahra’u Nasir ta rawaito gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ziyarci wajen da ake ajiyar kayan kariyar cutar Corona.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!