Labaran Kano
An bude masallacin jumu’a na marigayi Umar Sa’id Tudunwada
![An bude masallacin marigayi Umar Sa’id Tudunwada](https://freedomradionig.com/wp-content/uploads/2019/10/Umar-Said-Tudunwada.jpg)
A jiya jumu’a ne aka bude masallacin jumu’a na Umar Sa’id Tudunwada dake gidan rediyon manoma a unguwar Tukuntawa dake nan Kano.
Wazirin Kano, Mallam Sa’ad Shehu Gidado shine ya jagoranci bude masallacin, wanda ya samu halartar dubunnan al’umma daga sassa daban-daban na jihar Kano.
An sanyawa masallacin sunan marigayi Umar Sa’id Tudunwada tsohon shugaban tashoshin Freedom Radio sakamakon irin gudummuwar da ya baiwa aikin jarida.
RUBUTU MASU ALAKA:
Kungiyoyi sun yi zanga-zanga a Kano
Matakan Gwamnatoci sun kasafta fiye da biliyan 600