Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Mahaifi yaki karbar gawar dansa tsawon shekaru 20 a Kano

Published

on

Mahaifi yaki karbar gawar dansa tsawon shekaru 20 a Kano

Wani magidanci mai suna Shu’aibu Ahmadu mazaunin unguwar Brigade dake nan Kano, yaki karbar gawar dansa mai suna Auwalu Shu’aib da ya rasa ransa tsawon shekaru 20 da suka wuce.

Ana zargin matashin dan nasa ya rasa ransa ne sanadiyar wani sufeton ‘yan sanda mai suna Kwanta-Kwanta tun a wancan lokacin.

Dattijo Shu’aibu Ahmadu ya shaidawa shirin Indaranka na nan Freedom Radio cewa yaki amincewa ya karbi gawar dan nasa ne, domin neman ayi masa adalci bisa yadda dan nasa ya rasa ransa.

A jiya jumu’a ne dai asibitin kwarraru na Murtala Muhammed dake nan Kano ya bada sanarwar cewa har izuwa wannan lokaci gawar matashin tana nan kuma suna cigaba da kula da ita.

Allah ya kyauta.

RUBUTU MASU ALAKA:

An bude masallacin jumu’a na marigayi Umar Sa’id Tudunwada

Kungiyoyi sun yi zanga-zanga a Kano

Matakan Gwamnatoci sun kasafta fiye da biliyan 600

Tasirin talla ga ‘ya’ya Mata

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!