Labarai
An bude Sabon Masallaci a Rangaza Inkyan
An bude sabon Masallacin Kamsussalawati, a unguwar Rangaza Inkyan dake Layin Mai Garin Rangaza a Karamar hukumar Ungogo.
Masallacin wanda wani matashi kuma dan Kasuwa, Alhaji Salisu Yahaya Bagobiri, ya Gina, an samar dashi ne ga Al’ummar yankin don cigaba da gudanar da Ibada.
Da yake jawabi, ga Freedom Radio, jim kadan bayan kaddamar da Masallacin, daya daga cikin Jagororin matasan yankin, Mustapha Abdullahi Kwamred, ya bukaci Attajirai da masu hali a cikin Al’umma dasu cigaba da tallafawa jama’a ta hanyoyin daban-daban, musamman wajen yin Sadakatul Jariya ta hanyar ciyarwa ko hidimtawa Addini.
“Matashin ya saka Danba, ga Al’umma musamman ma masu Hannu da Shuni, kasancewar ba Hidimtawa Addini kadai ya tsaya ba, har ma da taimakawa Marayu da Marasa Galihu,” inji Mustapha Abdullahi.
You must be logged in to post a comment Login