Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An ceto mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Jigawa a Kano

Published

on

Ƴan sanda sun kuɓutar da mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya Hajiya Fatima Ibrahim daga hannun masu garkuwa a Kano.

Jami’in yaɗa labaran ƴan sandan jihar Jigawa Lawan Shisu Adamu ne ya tabbatar da hakan ga tashar Freedom Radio da ke Dutse.

Shisu ya ce, an ceto Hajiya Fatiman ne a rukunin gidajen Ɗanladi Nasidi da ke ƙaramar hukumar Kumbotso ta jihar Kano.

Sai dai bai yi ƙarin haske kan ko an biya kuɗin fansa, ko kuma an yi musayar wuta kafin kuɓutar da itan ba.

A yammacin Litinin ɗin da ta gabata ne wasu gungun ƴan bindiga suka yi awon ga da Hajiya Fatiman, a gidanta da ke unguwar Tsangayawa ta garin Kiyawa na jihar Jigawa.

Hajiya Fatima Ibrahim mahaifiya ce ga ɗan takarar Sanatan Jigawa ta tsakiya a jam’iyyar APC Alhaji Tijjani Ibrahim Gaya.

Ko a farkon watan Yunin da muke ciki ma, masu garkuwa sun sace mahaifiyar ɗan takarar Sanatan Kano ta tsakiya a jam’iyyar APC, Alhaji Abdussalam Abdulkarim Zaura.

Sai dai daga bisani jami’an tsaron farin kaya na DSS sun kuɓutar da ita a wani yanki na jihar Jigawa.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!