Labarai
An ci gaba da saurarar karar gwamnatin Kano kan ciyo bashi daga China
Babbar kotun tarayya da ke zaman ta anan Kano mai lamba uku karkashin mai shari’a Sa’adatu Ibrahim Mark, ta sanya ranar 19 ga watan gobe dan ci gaba da sauraron karar gwamnatin Kano kan yunkurin ta na ciyo bashin kudi sama da Biliyan 300 daga kasar China.
Tun da fari dai Kwamared Kabiru Sa’idu Dakata da kungiyar CAJA ne suka shigar suna kalubalantar gwamnatin kano dangane da yunkurin ciwo bashi daga kasar China.
Sai dai a zaman kotun na yau wasu lauyoyi su kimanin 10 karkashin farfesa Mamman Lawan Yusufari mai mukamin SAN sun bayyana a gaban kotun da takardu suna rokon kotun da ta sanya su a cikin shari’ar domin su kare shugaban majalisar dattawa.
Daga bisa ni an tafka muhawara tsakanin lauyan masu kara Barista Bashir Yusuf Tudunwuzurci da lauyan wadanda aka yi kara Barista M.N.Duru akan batun hurumin kotun ko tana da hurumin yin shari’ar ko akasin hakan.
Cikin wadanda akayi kara sun hadar da majalisar dokoki ta jahar kano da shugaban majalisar dattawa da babban bankin kasa CBN da ma’aikatar kudi da wani banki dake kasar China da kuma ofishin jakadanci na kasar ta China.
Wakilinmu Yusuf Nadabo Ismail ya zanta da lauyan masu kara Bashir Yusuf Wanda ya bayyana cewar ranto kudin da gwamnati ke son yi ana sa ran za a yi aikin jirgin kasa mai aiki da lantarki.
Shima lauyan gwamnati Barrister M.N.Duru yayi martani cikin harshen turanci, inda ya ce, kotu tana da karfin iko kan kowacce shari’a a don haka kotu zata duba bangarorin biyu don yanke hukunci.
Sai dai a zantawar Freedom Redio da Farfesa Mamman Lawan Yusufari mai Mukamin SAN Wanda shine lauyan shugaban majalisar dattawa ya ce, sun roki kotun da ta karawa sassan shari’ar lokaci dan yin nazari akan takardun karar.
You must be logged in to post a comment Login