Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Kannywood: Ana bukatar malamai da al’umma wajen gyaran fina-finai – Aminu Saira

Published

on

Wani mai shirya fina-finan Hausa a nan Kano Malam Aminu Saira, ya ce, idan har ana son gyara harkokin fina-finai to wajibi ne sai malamai da kuma al’umma sun shigo cikin lamarin domin samun gyaran da ya dace.

Aminu Saira ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da Freedom Radio, yana mai cewa yadda mutane suka yi watsi da lamarin fina-finan Hausa ne ya sanya a ke samun matsalolin da ake gani yanzu.

A cewarsa “Da mahukunta su shigo cikin harkokin shirya fina-finai da zuwa yanzu an gyaya duk wata barna da ake ganin ana yi a cikin masana’antar shirya fina-finan ta Kannywood.”

Aminu Saira ya kuma ce babban abinda ya sanya ake ganin masu shirya fina-finan kudancin kasar nan sun fi na arewa kokari shi ne yadda attajiransu ke taimaka musu da wasu abubuwa tare da daga su zuwa sama.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!