Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Musulmai na jimamin rasuwar Sayyada Rabi’atu Haruna

Published

on

Al’ummar musulmi daga sassan duniya daban-daban, na nuna jimamin su kan rasuwar mawaƙiyar nan mai begen Annabi Sallallahu alaihi Wasallam Sayyada Rabi’atu S. Haruna.

Babban shafin mabiya ɗariƙar Tijjaniyya a ƙasar nan wato Fityanul Islam na Facebook ne ya sanar da rasuwar mawaƙiyar da yammacin ranar Talata, inda ya ce tuni aka yi jana’izar ta.

Marigayiyar ta yi fice wajen rera waƙoƙin yabo na addinin musulunci.

Daga cikin fitattun waƙoƙin ta da suka shahara sun haɗa da, “Na yi dace, na riƙe soyayyar ma’aiki mai girma…” Da kuma “Sayyidin nasi, ya akramil khalƙi karimi…”.

Yanzu haka dai tuni kafafen sada zumunta suka cika da saƙonnin jimami da ta’aziyar ta.

Yayin da wasu kuma ke sanya wasu daga cikin waƙoƙin ta suna kewar ta.

Ga wasu daga ciki a nan:

Innalillahi wa inna ilaihiraji’un!

Allah ya yiwa Sayyida Rabi’utu S Haruna rasuwa wacce take rera yabon Shugaba (SAW)…

Posted by Muhammad Ahidan Bako Arifullah on Tuesday, 16 March 2021

Allah ya jikan Sayyida Rabi’atu S haruna mai kasidar yabon manzon Allah

Wacce tayi wakar ya zahrau fadima zuhuriyya…

Posted by Farouq Abdullahi Tukuntawa on Tuesday, 16 March 2021

Innalillahi wa Inna Ilaihin Raji’un!

Ashe Mawakiya Rabiatu Ta Rasu? Allah ya mata rahama. Ita tayi wakar nan ga Annabi…

Posted by Bilya Hamza Dass on Tuesday, 16 March 2021

Inna lillahi wa Inna ilaihi raji’un 😭💔

Allah ya Jikan Sayyida Rabi’atu S Harun ya gafarta Mata yasa aljanna ce makomarta

Ina fatan Allah ya sa da ta da ceton Abin qaunarta da yabo Annabi Muhammadu (S)😭🤲

Posted by Mai Dambun Naman Kaji on Tuesday, 16 March 2021

innalilahi wa inna ilayheer rajuu’unn 😭😭

allah ya jikan sayyada rabi’atu s haruna mai kasidar yaban manzon allah…

Posted by Youseep A Adam on Tuesday, 16 March 2021

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!