Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An daidaita tsakanin KAROTA da ‘yan kasuwa bayan dakatar da tsayawar Tireloli akan titi

Published

on

Al’umma a Kano sun jima suna zargin masu motocin daukar kaya na Tirela da haifar da cunkuoson ababen hawa a manyan kasuwanni da titunan jihar Kano.

Wanda hakan ke zama koma-baya ga kokarin da hukumomi ke yi na tabbatar da bin doka da oda, musamman ma a kan titunan, baya ga illar da hakan ke yi wa al’umma ta wajen gaza isa inda suke son zuwa a sakamakon cunkoso.

To amma wasu ‘yan kasuwar na ganin hakan sauki ne a gare su, musamman wajen samun saukin kashe kudi, domin kuwa idan manyan motocin suka tsaya daga wajen gari wurin da gwamnati ta samar zai sanya ‘yan kasuwar biyan karin kudi wajen shigowa da kayayyakin a kananan motoci.

Sai dai hukumar KAROTA ta ba da sanarwar cewar, daga ranar litinin mai zuwa 10 ga wannan wata na Agusta, za ta fara hana tsayawar manyan motocin a wasu yankunan kasuwannin Kano takwas.

Shugaban hukumar Baffa Babba Danagundi ne ya sanar da hakan, inda ya ce, motocin suna iya shigowa cikin dare, sannan baya ga hakan an hana manyan motocin tsayawa a kan titunan dake fadin jihar Kano.

Jin wannan sanarwar ta KAROTA ta sanya muka tuntubi wasu direbobin manyan motocin dake sauke kaya a wadannan kasuwanni, don jin ko yaya suka ji da wannan sanarwa? Nasir Ibrahim daya ne daga cikin direbobin wadannan manyan motoci, ya ce wannan mataki na KAROTA ya yi tsauri da yawa.

Sai dai ga ‘yan kasuwar kuwa cewa su ke ai tuni suka yi zama domin samun daidaito tsakaninsu da hukumar KAROTA, hasali ma sun cimma matsayar yadda za su ci gaba da sauke kayan amma ba tare da keta hakkin hanya ba.

Alhaji Ibrahim Dan-Yaro shi ne shugaban kwamitin dattijai na kasuwar Sabon Gari, kuma babban jigo a kasuwar Singa, ya ce sun cimma matsaya ta yadda duk ‘dan kasuwar da yake da wurin tsayawar mota ba tare da an shiga titi ba, to babu laifin in motar ta shigo ta tsaya a wannan wuri da ya tanada.

Alhaji Dan-Yaro ya ce, duk da wannan matsaya da suka cimma, amma dakatar da manyan motocin daga dibar kaya a kasuwannin ya fara shafar kasuwancin su domin kuwa a yanzu na cikin manyan kalubalen da suke fuskanta kasancewar hakan ya zama matsala ga bakin dake shigowa kasuwar domin yin kasuwanci.

Daga bisani Baffa Babba Danagundi ya tabbatarwa da Freedom Radio samun wannan daidaito a tsakaninsu.

Wannan na zuwa ne, makonni kadan bayan da KAROTA ta rushe wasu rumfunan wucingadi da kwantainonin kananan ‘yan kasuwa dake kasa kayayyaki a bakin tituna ba bisa ka’ida ba a wasu kasuwannin birnin Kano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!