Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Jigawa

An yi garkuwa da matar ‘dan majalisa a Jigawa

Published

on

Masu garkuwa da mutane sun kama matar Dan majalissar jiha mai wakiltar karamar Hukumar Gwiwa a jihar Jigawa.

Masu Garkuwar su 6, sun shiga garin Tsubut dake karamar hukumar Gwiwa da misalin karfe 3 na daren ranar Juma’a, inda suka shiga gidan Dan majalisar Hon. Aminu Zakari Tsubut, suka kuma tafi da matar sa Malama Ruakayya.

Wasu al’ummar garin sun ce masu Garkuwar sun nemi a basu kudi kafin su sako matar ta koma gidan mijinta.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Jigawa CP. Usman Sule Gwamna ya tabbatar da afkuwar lamarin, harma yace jami’an su na ci gaba da aikin bincike don ceto matar daga hanun masu Garkuwar.

Haka kuma ya bukaci al’umma su rika gaggawar kai rahoton duk wani motsi da basu gamsu da shi ba.

Wakilinmu Muhd Aminu Umar Shuwajo ya rawaito cewa wannan shi ne karo na biyu da masu Garkuwar da mutane suka dauki matan ‘yan majalisa a jihar, a cikin watan yuni ma sun dauke matar Dan Majalisar jihar mai wakiltar karamar hukumar Miga, kuma sai da aka biya kudi sannan suka sakota.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!