Labarai
An daure ‘yan Najeriya da dama a gidajen yarin kasar China saboda karewar takardun zaman su a kasar
Babban jakadan Najeriya a kasar China Mista Wale Oloko, ya ce ‘yan Najeriya da dama na daure a gidajen yari daban-daban a yankin Guangdong saboda samun su da laifin zama a kasar bayan takardun su na shiga kasar sun kare.
Mista Oloko ya bayyana hakan ne a jihar Lagos inda ya ce an kama wasu ‘yan Najeriya ne saboda aikata laifukan miyagun kwayoyi wanda ta kai ga har an tsare su a gidajen yarin baya ga wadanda aka kama da laiyukan da suka shafi rashin izinin zama a kasar.
A cewar babban jakadan a halin da ake ciki yawan ‘yan Najeriya dake zaune gidajen yarin kasar ta China sun kai dari shida 600, kuma babu tantama idan adadin su zai zarce hakan a gidan yarin Guangzhou, yayin da wasu da dama suka gwammace da a dawo da su gida Najeriya.
A don haka Mista Oloko ya yi kira ga ‘yan Najeriya da su daina kai ziyara wasu sassan kasar China saboda takardun su na izini shiga kasar ya kare kuma su yi biyayya ga dokokin hukumar shiga da ficen kasar.