Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Rikicin Gwamnatin Kano da Masarauta: Siyasa ko cigaba?

Published

on

YADDA DOKAR KAFA MASARAUTU TA SAMO ASALI

A ranar 8 ga watan Mayu na shekarar 2019 ne Gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje ya sa hannu a wata doka da ta bayar da damar kirkirar masarautu guda hudu daga masarautar Kano.

Kamar yadda tsohuwar majalisar ta Jihar Kano ta fada wata kungiya ce ta nemi a kirkiri sababbin masarautun wanda daga baya al’ummar masarautun suka zo majalisar ta dokokin jihar Kano suna masu goyon bayan kudurin majalisar ta jihar Kano na fito da sababbin masarautu.

Jim kadan bayan sakawa dokar kirkiro masarautun Karaye da Rano da Bichi da Gaya hannu Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya zagaya sababbin masarautun domin mika sandar kama Mulki ga sarakunan na Jihar Kano.

Gwamna Ganduje ya kuma tara sababbin Sarakunan a dakin taro na Sani Abacha inda ya mika musu takaddun kama aiki, duk wannan ya faru ne kafin ranar sake rantsar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a karo na biyu.

UMARNIN KOTUNA

A satin da aka fara rabawa sababbin Sarakunan sandar kama aiki ne  babbar Kotun Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da basu sanda inda wanda ya shigar da karar Rabi’u Gwarzo kuma Dan majalisa mai wakilitar yankin na Gwarzo ya shigar gabanta.

Amma duk da haka sai da gwamnatin ta Jihar Kano ta rabawa sababbin Sarakunan sanda sannan kuma ta cigaba da mu’amala da sauran Sarakunan na Karaye da Rano da Bichi da Gaya.

KIN BIN UMARNIN KOTU.

Bayan kammala rabawa Sarakunan sanda an cigaba da kai gwamnatin jihar Kano kara da ya hada da masu zaban Sarki.

Masu zaban Sarki da suka kai gwamnatin Jihar Kano kara sun hada da Madakin Kano Yusuf Nabahani da Sarkin Bai Mukhtar Adnan da Makaman Kano Sarki Abdullahi Ibrahim sai Sarkin Dawaki mai Tuta Bello Abubakar.

Masu zaban sarkin da suka kai gwamnatin ta jihar Kano kara yankunan su sun fada cikin sababbin masarautun da Gwamna Ganduje ya kirkira.

Kasar Madakin Kano wadda itace Dawakin Tofa ta fado karkashin sabuwar masarautar Bichi yayin da kasar Makaman Kano wato Wudil ta fada masarautar Gaya da kuma kasar Sarkin Dawaki mai Tuta itama ta fada masarautar Gaya, kasar Sarkin Bai ta Dambatta ta fada masarautar Bichi.

A ranar 21 ga watan Nuwamba ne babbar kotun Jihar Kano karkashin Usman Na’abba ta yanke hukunci inda tace sababbin masarautun ba’a yi su bisa ka’ida ba kuma ta rusa su nan take.

Bayan kwanaki Gwamnatin Jihar Kano ta sake mayar da kudurin neman kafa masarautu wanda bayan kwanaki kadan majalisar ta sahale da dokar ,Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sake saka mata hannu.

Ana tsaka da haka ne sai Gwamnatin Jihar Kano ta nada Sarki Muhammadu Sunusi II a matsayin sabon shugaban majalisar Sarakuna ta jihar Kano wanda ya dade bai amsa ba.

Sai da ta kai Gwamnatin Jihar Kano ta sake aikawa da Sarkin na Kano wasika inda ta umarce shi ko ya karbi mukamin shugaban majalisar Sarkunan na Kano ko akasin haka.

ZARGIN SHIGAR SARKIN KANO SIYASA.

Amma masana da masu sharhin al’amuran yau da kullum na alakanta kirkirar masarautu hudu a jihar Kano da siyasa, inda Gwamnatin jihar Kano ke zargin Sarkin Kano da daukar bangaranci lokacin zaben Gwamna na shekarar bana.

Ko a lokacin da hukumar zabe ta ayyana Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Jihar Kano a watan Maris din da ya gabata, sai da aka cire hoton mai marataba Sarkin Kano daga babban dakin taro na Coronation Hall dake gidan Gwamnati.

Dakin taron na Coronation Hall an gina shi ne musamman a shekarar 2014 domin bawa Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II sandar kamar aiki ,wacce akayi a ranar 7 ga watan Fabrairun Shekarar 2015 lokacin mulkin tsohon Gwamnan Jihar Kano Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso.

KIRKIRO SABABBIN MASARAUTU DOMIN CIGABA.

Duk da cewa mukamin Sarki mukami ne na kawa da kuma nuna al’ada da Addini da Tarihi ,Gwamnatin ta Jihar Kano karkashin Jagorancin Dr Abdullahi Umar Ganduje tace ta kirkiri sababbin masarutun ne domin kawo cigaba.

Amma masana al’amuran yau da kullum na ganin kirkirar masarautu ba cigaba zai kawo ba, sai dai rabuwar kai tsakanin al’ummar Jihar Kano baki dayan su wanda masarautun gaba daya ke karkashin jiha daya.

Har yanzu akwai wasu jihohi a arewacin kasar nan da suke da masarautu fiye da daya kamar su Jigawa da Niger da Bauchi da Nassarawa da Borno amma cigaban su bai kai na Jihar Kano ba.

Amma shi kansa Gwamna Abdulllahi Ganduje ya taba cewa zai gina manyan asibitoci a sababbin masarautun na Jihar Kano guda hudu.

Shin wadannan masarautu domin cigaba ne ko akasin haka, lokaci ne kawai zai iya bayyanawa?

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!