Kiwon Lafiya
An fara baiwa rundunar da ke yaki da manya laifuka horo na musamman a jihar Lagos
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta fara baiwa jami’an rundunar da ke yaki da manyan laifuka ta FSARS horo na musamman na makonni biyu a Jihar Lagos dangane al’amuran da suka shaf kare hakkin bil’adama.
A jiya Litinin aka fara baiwa ‘yan sandan FSARS din na fadin kasar nan wannan horo inda kwamandoji sama da 100 ke halarta don kara kwarewa kan yadda ya kamata su gudanar da aikinsu.
Yayin bude taron bada horon mataimakin babban Sufeton ‘yan sanda na kasa mai kula da shirin Emmanuel Inyang cewa ya yi taron bitar ya zama wajibi duba da irin korafe-korafen da al’umma ke yi na zargin take hakkil ‘dan’adam da jami’an ke yi.
Mista Inyang ya kuma gargadi ‘yan sandan su kaucewa cin zarafin jama’a, yana mai cewa karbar horon ya zama wajibi ga jami’an, kamar yadda fadar shugaban kasa ta bada umarni, don bunkasa aikin na su.
Sannan ya yi fatan za su yi amfani da horon da za su karba na makonni biyun wajen nuna kwarewa yayin gudanar da ayyukansu.
Kwamishinan ‘yan sanda mai kula da rundunar ta FSARS Halliru Gwandu ya ce aikin dakarun na sa ya takaita ne ga farautar ‘yan fashi da makami da masu garkuwa da mutane, baya ga wannan kuma babu wani nauyi da aka dora mu su.