Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Rundunar ‘yan sanda ta Kano zata daura dammara wajen yaki da shaye-shaye

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano Habu Sani Ahmad ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajan ganin ya kawar da dabi’ar nan ta shaye-shaye dake kara ta’azzara musamman a tsaknin matasa.

Habu Ahmad Sani ya bayyana hakan ya yin kaddamar da gangamin yaki da shaye shaye tsakanin matasa a fadin jihar nan bisa jagorancin Alhji Muntari Gashasha.

Kwamishinan ‘yan sanda ya kara da cewar zasu Fara gangamin wayar da kai ga daliban  makaratun sakandare da jami’o’i bisa ga ilar da shaye-shayen ke da shi.

A nasa bangaren Babban magatakardar kungiyar dalibai ‘yan kasar nan shiyar Arewa Abdullahi Muhammad Sale ya bayyana cewar zasu aiki da rundunar da kafada-da-kafada wajan yaki da shaye-shayen a makaratu.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar, kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano  Habu Sani ya baiwa kungiyar daliaban litattafai da fefen bidiyo dake nuna ilar shaye shayen.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!