Labaran Wasanni
An fara gasar Ahlan Cup a Kano
A jiya Lahadi ne aka bude gasar cin kofin shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano Alhaji Shariff Rabiu Inuwa Ahlan karo na uku a filin wasa na Sani Abacha dake Kano.
Manyan kungiyoyin kwallon kafa a Nigeria ne zasu fafata a gasar wadda aka raba zuwa rukuni hudu.
Rukunin A | Rukunin B | Rukunin C | Rukunin D |
Katsina United | Kano Pillars | Wikki Tourist | Enyimba |
Jigawa Golden Stars | Plateau United | Sokoto United | Rarara FC |
Lobi Stars | Rivers United | Kwara United | Elkanemi Warriors |
Abia Warriors | Yobe Desert | Pataskum Academy | DMD |
Nasarawa United | Kada City | Kano Selected |
Wannan dai shine karo na uku da shugaban hukumar kwallon kafa ta Jihar Kano ke shirya wannan gasa, wadda ake gudanarwa gabanin fara kakar wasanni ta Nigeria.
Da yake zantawa da manema labarai a yayin bikin bude gasar, Shugaban hukumar kwallon kafa ta jihar Kano Shariff Rabiu Inuwa Ahlan, ya ce, duk shekara suna shirya gasar don bai wa kungiyoyin wata dama su yi shiri na musamman don tunkarar kakar wasanni da za a shiga.
Sharu Ahlan ya kuma yi kira ga masu hannu da shuni musamman ma ‘yan kasuwa da su shigo su tallafa wajen bunkasa harkokin wasanni.
Harkar wasanni tafi karfin ace gwamnati ce kadai za ta yi komai, don haka akwai bukatar sauran mutane su shigo ciki musamman ma ‘yan kasuwa inji Sharu Ahlan.
A wasan farko na gasar da aka fafata kungiyar kwallon kafa ta Kano Pillars ta yi rashin nasara a hannun Plateau United da ci daya mai ban haushi.