ilimi
An fara gudanar da taron KANSIS25

An fara gudanar da taron Kano Social Influencers Summit na bana wanda cibiyar bunƙasa fasahar sadarwa da ci gaban Al’umma CITAD ke gudanarwa duk shekara karo na 6 watau KANSIS25.
Taron na KANSIS, wanda CITAD ta fara gudanarwa tun a shekarar 2019, ya na haɗa masana da dama daga sassa daban-daban na Najeriya inda ake tattaunawa musamman kan amfani da fasahar zamani wajen samar da ayyukan ci gaban al’umma.
Kamar yadda aka saba ana gudanar da taron ne na tsawon kwanaki biyu, inda na bana za a gudanar da shi a tsakanin yau Laraba da kuma gobe Alhamis a jami’ar Khalifa Isyaku Rabi’u da ke tsakiyar birnin Kano.
Haka kuma, taron na bana, zai mayar da hankali ne wajen ɗabbaka tsarin yin amfani da fasahar zamani mai amfani da tinanin Ɗan-adam watau AI.
You must be logged in to post a comment Login