Labarai
An gano littattafai masu shekara Dubu a Kano
An gano littattafai masu shekara Dubu a Kano
Ma’ajin cibiyar Abdullahi Mai Masallaci dake nan Kano Dr. Baba Uba Ringim ya bayyana cewa cibiyar tana da littatafai da suka kai shekaru dubu daya a Duniya.
Dr. Baba Uba Ringim ya bayyana hakan ne lokacin da yake tattaunawa da filin Barka da Hantsi.
Dr. Baba yace rashin mai da hankali wajen bincike ne yasa alummar Jihar Kano da na arewacin Najeriya basa amfana da cibiyar binciken ta Abdullahi mai Masallaci.
Yayi Kira ga al’umma da su rika amfani da damar ta cibiyar Abdullahi mai Masallaci wanjen nazari da fadada bincike domin inganta ilimi.
Ya kara da cewa Wanda ya assasa cibiyar ta Abdullahi mai Masallaci Alhaji Uba Ringim ya siyo wa cibiyar littatafai daga kasar Masar Wanda aka rika kawo su ta jirgin ruwa.
Haka kuma masu bukatar amfani da cibiyar kan yi tsawon shekara guda idan suka biya Naira hamsin kacal.
Dr. Baba yace cibiyar da take Sabuwar Kofa a bayan makarantar koyan harshen Larabci zata taimaka gaya wajen habaka ilimi anan Jahar Kano.
Rahoto: Abbas Yusha’u Yusuf