Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

An gano maboyar sindarin da ya haifar da cututtuka a Kano

Published

on

Gwamnatin jihar Kano ta gano maɓoyar wani sinadarin haɗa lemo da ake zargin shi ya haddasa wata cuta da ta jikkata mutane da dama tare da asarar rai.

Shugaban hukumar kare masu sayen kaya ta Kano Baffa Babba Ɗanagundi ne ya bayyana hakan ga Freedom Radio.

Baffan ya ce, an gano maɓoyar ne a wani gida da ke ƙaramar hukumar Minjibir.

A cewar sa, an samu buhu ɗari uku da tamanin na sinadarin kuma sun cafke wasu mutane da ake zargi.

Ana zargin dai yin amfani da sinadarin wanda wa’adin amfani da shi ya ƙare ya haifar da cuta ga al’umma a wasu yankunan Kano.

Ya zuwa yanzu dai yankunan da al’amarin ya shafa sun haɗa da ƙaramar hukumar Gwale da Nassarawa da Birni da Kewaye, sai ƙaramar hukumar Tarauni da Bunkure.

A na sa ɓangaren Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr. Aminu Ibrahim Tsanyawa ya shaidawa Freedom Radio cewa tuni suka shiga bincike kan lamarin.

An kuma samar wurare na musamman domin kula da masu cutar, waɗanda suka haɗa da asibitin kula da cututtuka masu yaɗuwa da aka fi sani da asibitin Zana, da kuma asibitin garin Rano.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!