Labarai
An gurfanar da Buhari gaban kotu kan ciyo bashi
Kungiyar tabbatar da gaskiya da daidaito a ayyukan gwamnati (SERAP) ta gurafanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja, tana bukatar kotun ta haramta musu ciyo bashi daga asusun ‘yan Nigeria da suka jima ba su yi amfani da shi ba.
Kudaden da gwamnati ke son ciyo bashinsu daga asusun ajiyar banki na ‘yan kasa wadanda suka jima ba su yi amfani da su ba, sun kai naira biliyan dari takwas da miliyan casa’in da biyar.
Cikin takardar karar mai lamba FHC karan-tsaye ABJ karan-tsaye CS karan-tsaye 31 karan-tsare 2021, mai kuma dauke da sa hannun lauyoyin kungiyar ta SERAP Kolawale Oluwadare da Adelanke Aremo ta bukaci kotun da ta haramta daukar wannan mataki da gwamnati shugaba Buhari ke shirin yi.
Kungiyar ta SERAP ta ce taba kudaden ya sabawa doka, a don haka ta ce, ba daidai bane gwamnatin tarayya ta ciyo bashi daga cikin asusun ajiya na jama’a ba tare da amincewar su ba.
Sauran wadanda kungiyar ta SERAP ta sanya cikin wadanda ta ke kara akwai: gwamnatin tarayya, da attorney janar na kasa kuma ministan shari’a Abubakar Malami, shugaban majalisar dattijai Sanata Ahmed Lawan, da takwaransa na wakilai Femi Gbajabiamila da kuma ministar kudi, kasafi da tsare-tsare Zainab Ahmed.
You must be logged in to post a comment Login