Manyan Labarai
An kaddamar da kotun daukaka kara a Kano
Daga Aminu Halilu Tudun Wada
Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya aza harsashin kaddamar da fara ginin kotun daukaka kara wato appeal court na nan jiha da gwamnatin Kano ta bada filin ginin a harabar sakatariyar Audu Bako.
Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda yake tare da gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar, shi ne ya aza harsashin ginin a safiyar yau tare da babban jojin jiha mai shari’a Nura Sagir .
Sarki Sanusi II ya taya Ganduje murnar samun nasara a Kotu
Kotu ta fara sauraron shari’ar maita a Kaduna
Da yake jawabi kafin aza harsashin ginin gwamna Ganduje, yace gwamnatin sa tare da hadin gwiwar takwarar ta, ta Jigawa zasu yi duk mai yiwuwa tare da daukar nauyin ginin Kotun, don ganin an saukakawa masu shigar da kara na jihohin biyu da wasu jihohin arewacin kasar nan , don haka gwamnatin sa ta bada filin gina Kotun.
Da take nata jawabin shugabar Kotun daukaka kara ta kasa mai Shariah Zainab Bulkachuwa, tace gwamnatin tarayya ta ga dacewar kafa sababbin kotunan ne a yankuna da ban -da ban na kasar nan don takaita hukunce hukuncen da suke a kasa da cunkuson kurkuku na kasar nan, da kuma rage yawaitar kashe kudaden shigar da kara ga masu korafi ko kara.
Dumbin Alkalai da masu shari’a daga sassan kasar nan ne suka halarci taron aza harsashin gina Kotun wanda aka kaddamar , an kuma sakawa ginin Kotun sunan Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa.