Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Covid19: Ana dab da kammala ginin cibiyar killacewa da Dangote ke ginawa a Kano

Published

on

Gidauniyar Aliko Dangote tare da nadin gwiwar Gwamnatin Kano ta ce a gobe ne ake sa ran za’a kammala aikin ginin cibiyar killace masu cutar Corona Virus da ke filin wasa na Sani Abacha a Kano.

Manajan shirye shiryen gidauniyar ta Aliko Dangote Foundation Sanusi Ahmad Abdulkadir ne ya bayyana hakan a lokacin da Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kai ziyarar duba yadda aikin ginin cibiyar ke gudana.

Ya ce kasancewar yanzu an samu nasarar kammala bangare daya na maza a gobe ne ake saran kammala daya bangaren cibiyar.

LABARAI MASU ALAKA

Gwamnatin Kano ta fara feshin maganin cutar Covid-19

Covid-19: An takaita zirga-zirga a kasuwar kantin Kwari

Da yake jawabi bayan kammala duba aikin, Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya jinjinawa gidauniyar Dangote bisa samar da cibiyar mai dauke da gadaje 500 wanda yake dauke bangaren mata mai gadaje 250 da bangaren maza mai gadaje 250.

Wakiliyar mu ta fadar Gwamnatin Kano Zahrau Nasir ta ruwaito cewa Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dr Aminu Ibrahim tsanyawa ya ce sun dauki dukkan matakan tabbatar da tsaftace cibiyar don samar da ingantacciyar lafiya ga Marasa lafiyar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!