Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

An kaddamar da kotun daukaka kara a Kano

Published

on

Daga Aminu Halilu Tudun Wada

Gwamnan jihar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya aza harsashin kaddamar da fara ginin kotun daukaka kara wato appeal court na nan jiha da gwamnatin Kano ta bada filin ginin a harabar sakatariyar Audu Bako.

Dr Abdullahi Umar Ganduje, wanda yake tare da gwamnan jihar Jigawa Alhaji Badaru Abubakar,  shi ne ya aza harsashin ginin  a safiyar yau tare da babban jojin jiha mai shari’a Nura Sagir .

Sarki Sanusi II ya taya Ganduje murnar samun nasara a Kotu

Kotu ta fara sauraron shari’ar maita a Kaduna

Da yake jawabi kafin aza harsashin ginin gwamna Ganduje, yace gwamnatin sa tare da hadin gwiwar takwarar ta,  ta Jigawa zasu yi duk mai yiwuwa tare da daukar nauyin ginin Kotun, don ganin an saukakawa masu shigar da kara na jihohin biyu da wasu jihohin arewacin kasar nan , don haka gwamnatin sa ta bada filin gina Kotun.

Da take nata jawabin shugabar Kotun daukaka kara ta kasa mai Shariah  Zainab Bulkachuwa, tace gwamnatin tarayya ta ga dacewar kafa sababbin kotunan ne a yankuna da ban -da ban na kasar nan don takaita hukunce hukuncen da suke a  kasa da cunkuson kurkuku na kasar nan, da kuma rage yawaitar kashe kudaden shigar da kara ga masu korafi ko kara.

Dumbin Alkalai da  masu shari’a daga sassan kasar nan ne suka halarci taron aza harsashin gina Kotun wanda aka kaddamar , an kuma sakawa   ginin Kotun sunan Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!