Labarai
An kai mummunan hari a hanyar Kano zuwa Kaduna
An dauki wannan hoton a shekarar 2019 lokacin da direbobi suka tare hanyar Kaduna zuwa Abuja sakamakon kisan wani direba.
Rahotonni daga jihar Kaduna na cewa wasu ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane sun kai hari a yankin Fandisho dake mararrabar Jos, kan hanyar Kano zuwa Kaduna.
Shaidun gani da ido sun shaidawa Freedom Radio cewa, da misalin karfe goma na daren jiya Talata ne yan bindigar suka tare hanyar, sa’annan suka farwa matafiya, inda ake zargin sun yi garkuwa da wasu daga cikin matafiyan, bayan da suka budewa wasu wuta.
Kazalika, mazauna garin sun shaidawa Freedom Radio cewa, maharan sun dauki tsawon lokaci kafin su bar kan hanyar duk da daukin da jami’an tsaro suka kai musu.
Har ila yau, al’ummar garin Kaduna sun wayi gari da ganin zirgar-zirgar motocin bada agajin gaggawa, dana hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa na jigilar wadanda lamarin ya shafa zuwa asibitin sojoji na bataliya ta 44 dake jihar Kaduna.
Wakilin Freedom Radio a Kaduna Haruna Ibrahim Idris yayi kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kaduna DSP, Yakubu Sabo kan afkuwar lamarin amma abin yaci tura.
Akwai yiwar sake kai hari a Sakandiren ‘yan mata na Dapchi
Boko haram:sun kai hari kauyukan da kan iyakan jihohin Adamawa da Borno a jiya
Kungiyar boko haram ta kai hari karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa
Kazalika, wakilin namu yayi kokarin jin ta bakin hukumar kiyaye afkuwar hadura ta kasa shiyyar Kaduna amma hakonsa bai cimma ruwa ba.
Har ila yau, mazauna garin Mararrabar Jos sun shaidawa Freedom Radio cewa ko a satin da ya gabata, masu garkuwa da mutane sun tsare hanyar inda suka yi garkuwa da mutane kimanin goma sha biyar.
Haka kuma, a makon da ya gabata, wasu gun-gun masu garkuwa da mutane sun afkawa titin zuwa Birnin Gwari ya dangana kauyen Uduwa zuwa Buruku inda suka yi garkuwa da mutane kimanin sittin ciki har da wani babban malamin Kirista a yankin.