Labarai
An kama dan shekara 23 ya hadiye kullin tabar iblis guda 59

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA ta kama wani mutum mai suna Okoguale Douglas a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja dauke da tabar iblis da nauyinsa ya kai gram 781.2.
A cewar NDLEA mutumin mai shekaru 23 ya hadiye tabar iblis din ne kulli 59 a cikinsa, a kokarinsa na safararta zuwa birnin Milan da ke kasar Italiya.
Hukumar ta NDLEA ta kuma ce da zaran ta kammala bincike za a gurfanar da shi gaban kotu.
You must be logged in to post a comment Login