Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Tsaro: Sojoji sun kai sumame masallaci da wasu gidaje a Hotoro

Published

on

Jami’an soji sun kai sumame unguwar Hotoro filin Lazio da ke nan Kano.

Mazauna unguwar sun shaidawa Freedom Radio cewa, sojojin sun dira unguwar ne, yayin da ake tsaka da shan ruwa inda suka mamaye wani masallacin kamsu salawati.

Sojojin sun yi awon gaba da wasu magidanta a unguwar da kuma wasu da aka samu a masallacin da wani kango mai maƙotaka da shi.

Aƙalla mutane sama da 10 ne mazauna unguwar suka ƙiyasta sojoji sun kama a yayin sumamen.

Masallacin mallakar wasu ƴan jihar Borno ne da suka yo gudun hijira zuwa nan Kano.

Freedom Radio ta so jin ta bakin wasu matan waɗanda aka kama mazajensu amma ba su amince ba.

Sai dai wasu shaidun gani da ido sun ce, jami’an sojin sun kama wasu abubuwa da ba a tantance ba a wani kango da ke kusa da masallacin.

Freedom Radio ta yi ƙoƙarin jin ta bakin rundunar sojin a nan Kano amma har kawo lokacin da muke haɗa wannan rahoto haƙan mu bai cimma ruwa ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!