Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Manyan Labarai

Mun kama Sarkin mayu na bogi-Muhiyi Magaji

Published

on

Hukumar karbar Korafe-Korafe da Yaki da cin hanci Da Rashawa Ta Jihar Kano ta chafke sarkin Na Albasu Yahaya Wanzam wato sarkin Mayu bisa Yadda Yake Fakewa Da Guzma Yana Harbin Karsana.

Shugaban hukumar ta jihar Kano Muhiyi Magaji Rimingado ne ya bayyana hakan a yayin da yake ganawa da wakilin mu Nasiru Salisu Zango bayan kama wanda ake zirgi.
Hukumar ta karbar Korafe-Korafe da Yaki da cin hanci da rashawa na zargin wanzamin da yaudarar wasu mutane Ashiri 20 da cewa su Mayu ne yana karbar kudi a hannun su da zummar warka da su.

Ana dai zargin Mal Yahaya Wanzam da yaudarar mutanen bayan da kwashe kusan shekaru uku yana cewa su Mayu ne alhalin ba haka ba tun yake ba hasali ma ko kada bai yi ba.

Da yake jawabi shugaban hukumar ta karbar korafe-korafe da yake da cin hanci ta jihar Kano yace sun Kari korafe korafen mutane ne daga bisani kuma suka zurfafa bincike kuma tuni wanda ake zargin yake hannun su

Ku biyo cikin shirin Inda ranka don jin cikakken labarin

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!