Ƙetare
An kama sojojin da ake zargi da da shirya juyin mulki a Mali

Rahotonni daga gwamnatin mulkin soji a kasar Mali sun ce, an kama sojoji kusan talatin bisa zargin su da hannu a shirin kifar da gwamnatin kasar.
Wasu majiyoyin tsaro sun ce waɗanda aka kama sun haɗa da Janar Abass Dembele, tsohon gwamnan yankin Mopti a tsakiyar ƙasar.
Kafar yada labarai ta BBC ta ruwaito cewa har zuwa lokacin da ta fitar da rahoton, gwamnatin sojin kasar ba ta ce komai ba a hukumance.
Haka kuma ta ruwaito cewa, Zarge-zargen yunƙurin kifar da gwamnati na nuna ƙaruwar zaman ɗar-ɗar a tsakanin gwamnatin sojin inda rahotanni ke cewa matsalar masu iƙirarin Jihadi na ƙara faɗaɗa a arewacin ƙasar ta Mali.
You must be logged in to post a comment Login