Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

An kamo ƴan bindigar da suka yi garkuwa da ɗaliban Greenfiel da Bethel Baptist – yan sanda

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kaduna ta samu nasarar cafke ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da daliban makarantar Greenfield da kuma na Bethel Baptist da ke karamar hukumar Chikun a Jihar Kaduna.

Haka zalika ‘yan sandan sun kama ‘yan bindigar da suka yi garkuwa da da dalibai 37 na Kwalejin nazarin harkokin tsirrai ta Afaka da ke karamar hukumar Igabi.

Mai magana da yawun rundunar ASP Muhammad Jalige ne ya tabbatar da hakan jiya, lokacin da yake holin mutanen da aka kama a shelkwatar yan sandan Jihar.

Jalige ya ce daga cikin wadanda suka kama har da wani mai suna Usman ‘dan asalin karamar hukumr Bukuyum da ke Jihar Zamfara, wanda suka ce ya shahara wajen garkuwa da mutane.

 

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!