Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kamo ɗaurarru 8 da suka tsere daga gidan yarin Jos

Published

on

Rundunar yan sandan jihar Filato ta tabbatar da kamo ɗaurarru takwas cikin wadanda suka tsere daga gidan gyaran hali na Jos sakamakon harin da ƴan bindiga suka kai wa gidan.

Mai magana da yawun rundunar ASP Ubah Ogaba ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya bayar a safiyar Litinin ɗin nan.

ASP Ubah Ogaba ya ce, bakwai daga cikin ɗaurarrun yan sanda ne suka samu nasarar kamo su, yayin da guda daga ciki ya miƙa wuya da kan sa.

A jiya lahadin ne wasu ƴan bindaga suka kai farmaki gidan gyaran hali a Jos, lamarin da yayi sanadiyyar tserewar wasu daga cikin ɗaurarru.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!