Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna na kokarin zamanantar da yanayin aiki a jihar nan da watan Disamba

Published

on

Gwamnatin jihar Kaduna, ta rage ranakun ayyukan gwamnati a jihar zuwa kwana 4 a wani mataki na garambawul da maida aikin gwamnatin zuwa wani mataki na zamani.

A wata sanarwa da Mai Baiwa Gwamnam jihar shawara kan harkokin yada labarai Muyiwa Adekeye ya fitar, ya ce daga yanzu ranakun aiki a jihar sun koma Litinin zuwa Alhamis, daga karfe 8 na safe zuwa 5 na yamma.

Wannan dai wani mataki ne na baiwa Ma’aikata damar hutawa da iyalansu da kuma basu damar gudanar da harkokin noma.

Muyiwa ya ce shirye-shirye sun yi nisa domin ganin su ma fannin ma’aikatu masu zaman kansu sun bi wannan sabon salon aiki.

Sai dai kuma gwamnati tace wannan tsari banda ma’aikatan fannin ilimi da lafiya da sauran ayyukan daya zama dole a gudanar da su.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!