Labarai
An karrama jami’in KAROTA saboda ƴaƙar masu ƙwacen waya
Ƙungiyar jama’ar Arewacin ƙasar nan masu amfani da kafafen sada zumunta sun karrama wani jami’in KAROTA.
An karrama jami’in KAROTAr mai suna Abubakar Ibrahim Mukhtar ne sakamakon ƙoƙarin da yayi na cafke wasu masu ƙwacen waya a titin ɗanagundi.
Ƙungiyar ta bai wa jami’in lambar yabo da kuma kyautar kuɗi har naira dubu ɗari da goma.
Shugaban ƙungiyar Malam Ibrahim Sanyi-Sanyi ya ce, sun karrama matashin ne domin ya zama abin koyi ga na baya.
Shugaban hukumar ta KAROTA Baffa Babba Ɗanagundi ya yi godiya ga ƙungiyar inda ya ce, ita ma hukumar ta yi nisa wajen shirin karrama shi.
Haka ma ƙungiyar ta karrama Bashir Sharfaɗi na Freedom Radio da lambar yabo bisa rahoton da yayi kan matashin, wanda ya ɗauki hankulan jama’a da dama.
You must be logged in to post a comment Login