Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

An kashe jami’an ‘yan sanda sama da 20 a watan Maris – Muhammad Adamu

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta ce akalla jami’anta ashirin ne suka rasu sakamakon harin ‘yan ta’adda a watan maris din daya gabata.

Babban Sufeton ‘yan sandan kasar nan Muhammad Adamu, ne ya bayyana hakan yayin wani taron tuntuba na masu ruwa da tsaki kan sha’anin tsaro.

Muhammad Adamu ya ce an aikata laifukan kisan kai akalla guda dari da talatin da bakawai da laifukan satar mutane guda dari da goma sha tara a watan na Maris.

Ya kuma bukaci al’ummar da su ci gaba da bawa jami’an tsaro hadin kan da ya kamata domin kawar da hanyoyin aikata laifukan ta’addanci da fashi da makami a kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!