Connect with us

An Tashi Lafiya

An kashe shuguban ƙungiyar ISWAP Abu Musab Al-Barnawi

Published

on

Rahotanni sun ce an kashe shugabann kungiyar ISWAP Abu Musab Al-Barnawi a Jihar Borno, ɗaya daga cikin kungiyoyin dake kai munanan hare-hare suna kashe jama’a a yankin Tafkin Chadi.

Bayanan sun ce an kashe Abu Musab Al-Barnawi ne, a ƙarshen watan Agustan da ya gabata kamar yadda wasu majiyoyi suka tabbatar.

Wasu rahotanni masu karo da juna sun nuna cewa, sojojin Najeriya ne suka kashe shi, yayin da wasu majiyoyi kuma ke cewa a rikicin cikin gida ya mutu.

Ya zuwa yanzu dai, sojojin Najeriya basu sanar da kashe shugaban na kungiyar ISWAP ba, kamar yadda shafin rfi ya rawaito.

Al-Barnawi ɗa ne ga Muhammadu Yusuf, mutumin da ya kafa kungiyar boko haram kafin jami’an tsaron Najeriya su kashe shi a shekarar 2009 lokacin da ya kaddamar da yaki akan su, abinda yayi sanadiyar mutuwar akalla mutane sama da dubu guda a lokacin.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a Reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!