Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Mun amince da kashe kwamandojin yaki a tafkin Chadi – ISWAP

Published

on

Sabon shugabannin kungiyar ISWAP ta yammacin afirka  ya ce sun amince da kashe wasu manyan kwamandojin kungiyar guda uku.

Rahotanni sun ce cikin wadanda za a kashe har da babban kwamandan kungiyar da ya yi kaurin suna wajen jagorantar hare-haren ta’addanci a yankin tabkin Chadi, wato Amir Baba-Kaka.

Haka zalika kungiyar ta ISWAP ta kuma kashe Ba’a Masta wanda babban kwamada ne kuma malami na kungiyar.

Wata majiya ta ce alkalin kotun kungiyar ta’addar ya samu kwamandojin da aikata laifuka da suka hada da: rashin bin umarnin uwar kungiyar da rashin adalci da cin hanci da rashawa da wadaka da dukiyar kungiyar da kuma kashe-kashen cikin gida tsakanin mambobin kungiyar.

Haka zalika bayanai sun ce kungiyar ta ISWAP ba ta ji dadin yadda manyan kwamandojin nata suka gaza wajen kare hare-haren da dakarun kasar nan suka kai wa ‘yan kungiyar ba, da yayi sanadiyyar mutuwar kwamandojin kungiyar da dama.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!