Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

An kone dubban Sinadaran hada lemo na Jolly Jus a Kano

Published

on

Ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta kone Sinadrin harhada lemo na Jolly Jus kimanin katan dubu ashirin da takwas da dari uku da ashirin da biyu,wanda wa’adin amfaninsa zai kare nan da watanni shida bisa sahallewar kamfanin

Kwamishinan lafiya na jihar Kano Dakta Aminu Ibrahim Tsanyawa ne ya jagoranci kona kayan a shalkwatar hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta jihar kano da yammacin yau Alhamis.

Kwamishinan ya yabawa kamfanin nisa yadda suka baiwa hukumar kayan domin ta kona, domin kare lafiyar al’umma.

Da yake jawabi wakilin kanfamin da ke hada sinadarin lemo na Jolly Jus Yahaya Isa Abdurrashid ya ce kamfanin ya kara siyo kayan ne a hannun abokan huldarsu saboda gudun karsu siyar idan wa’adinsa ya kare.

Wakiliyar mu Aisha Shehu Kabara ta ruwaito cewar Kwamishinan lafiya na jihar Kano ya ja hankalin mutane da su cigaba da sanya takunkumin rufe baki da hanci da wanke hannu da kuma kiyaye dokokin cutar Corona domin kuma har yanzu akwai sauranta.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!