Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Ganduje ya nemi Buhari ya sake yin nazari kan yadda ake rabon arzikin kasa

Published

on

Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bukaci gwamnatin tarayya ta sake yin nazari kan yadda ake rabon arzikin kasa.

Kwamishinan kananan hukumomi na jihar Kano Murtala Sule Garo ne ya bayyana hakan a yau lokacin da yake zantawa da manema labarai ya yin gudanar da taron bita ga shugabannin kananan hukumomi da hukumar dake rarraba arzikin kasa ta shirya a fadar gwamnatin Kano

Alhaji Murtala Sule Garo ya kara da cewa in akayi gyara a yadda ake rabon to Babu shakka hanyoyi da ilimi da noma tare da harkar lafiya zasu Kara samun ingantuwa la’akari da cewa gwamnatocin kananan hukumomi da na jiha su suka fi kusa da alumma da Kuma sanin matsalolin su

Ya Kara da cewa makasudin taron bitar shi ne don a fadakar da shugabannin kananan hukumomi yadda zaa inganta hanyoyin samun kudin Shiga

Wakiliyar mu Zahrau Nasir ta ruwaito cewa kwamishinan na kananan hukumomin na Kano ya kuma ce taron bitar ya Kuma mayar da hankali wajen tattauna hanyoyi da dabarun da zaa bi don inganta harkokin al’umma a fadin jihar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!