Kiwon Lafiya
An kori jami’an rigkafin Shan Inna su 12 a Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta kori wasu jami’an bada allurar rigakafin shan-inna su 12 sakamakon samun su da laifin karya dokokin bayar da allurar allurar da suka yiwa wasu ‘yara yayinda ake gudanar da shirin.
Jami’in lura da asibitin sha ka tafi da ke yankin karamar hukumar Tarauni a nan Kano, Malam Nura Haruna ne ya tabbatar da hakan, lokacin da yake ganawa da manema labarai a nan Kano.
A cewar sa ma’aikatan sun sanya shaidar yiwa yara rigakafin allurar ta Polio da aka saba yiwa kananan yara bayan sun karbi allurar, inda aka gano cewa yaran da aka sanya musu wannan alamar ba’a yi musu rigakafin ba.
Nura Haruna ya tabbatar da cewa jami’an aikin allurar rigakafin an same su da laifin hada baki da iyayen yaran da basa son a yiwa ‘yayan su rigakafin, inda suka diga musu tawadar da ke nuna alamar an yiwa yaro allurar, alhalin ba hakan bane.
Jami’in kiwon lafiyar ya kuma bayyana cewa abinda gwamnatin Kano ta sanya a gaba shi ne kakkabe matsalar Polio a fadin jihar baki daya, kuma ba zata yi kasa a gwiwa ba wajen daukar mataki kan duk wanda aka samu yana yiwa shirin gwamnatin jihar makarkashiya.