Connect with us

Coronavirus

Corona: A ci gaba da yiwa jama’a rigakafin Astrazeneca – WHO

Published

on

Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO ta ba da umarnin ci gaba da amfani da allurar riga kafin Cutar Corona, duk ‘yan matsalolin da allurar ke da ita.

kwamitin kula da allurar riga kafin ne ya ba da wannan umarnin kan cewa a ci gaba da amfani da ita, kuma allurar a yanzu haka tana rage yaduwar cutar corona.

Ya na mai cewa, ita allurar tana kare garkuwar wanda aka yiwa, da wadanda ke kusanci ga wanda aka yiwa.

A cewar kwamitin, idan har aka samu matsala ga wanda aka yiwa, to dama can akwai abunda ya ke damun wanda aka yiwa, bai magance shi bat un da fari.

Idan za a ya tunawa dai, ko a ranar Litinin din nan data gabata, wani ma’aikacin lafiya a kasar Norway ya rasu jim kadan bayan ya karbi allurar kuma wasu mutane uku daban an kwantar da su Asibiti sakamakon allurar.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!