Labarai
An kori shugaban NNPP Hashimu Dungurawa daga mukaminsa
Shugabannin zartarwa na jam’iyyar NNPP a mazabar Gargari, da ke Ƙaramar Hukumar Dawakin Tofa a Kano, sun kori Shugaban Jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashimu Dungurawa, daga jam’iyyar.
Matakin ya biyo bayan kudurin da mambobin zartarwa 27 na mazabar suka amince da shi, a yayin wani taron zartarwa na biyu da aka gudanar makonni biyu bayan sake zabensa.
Taron dai, ya gudana ne ƙarkashin jagorancin Shugaban mazabar Shu’aibu Hassan tare da Sakataren ta, Yahaya Sa’idu Dungurawa.
A cewar shugabannin, an tsige Hashimu Dungurawa ne bisa zarginsa da haddasa rarrabuwar kai a cikin jam’iyya, tayar da rikice-rikicen cikin gida, gazawar biyan kudaden jam’iyya, da kuma furta kalaman batanci ga Gwamnan Jihar Kano.
Shugabannin ward din sun bayyana cewa irin wadannan ayyuka sun sabawa ka’idojin jam’iyya, kuma suna lalata martaba, hadin kai da cigaban NNPP a jihar.
Sun jaddada cewa an dauki matakin ne cikin bin kundin tsarin mulkin jam’iyyar, domin tabbatar da da’a, zaman lafiya da hadin kai a cikin jam’iyyar.
Haka kuma, sun ce an aika kwafin kudurin tsige shi zuwa ga shugabannin jam’iyyar a matakan Karamar Hukuma, Jiha da kuma Kasa, domin daukar matakan da suka dace.
Bugu da kari, an sanar da jagoran jam’iyyar NNPP na kasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kuma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, domin sani da bayar da umarnin da ya dace.
Shugabannin mazaɓar ta Gargari, sun ce wannan mataki zai zama izina ga duk wanda ke amfani da mukaminsa ba bisa ka’ida ba, ko kuma yake ganin ya fi dokoki da ladabtarwar jam’iyya karfi.
A karshe, sun sake jaddada biyayyarsu ga shugabancin NNPP na kasa karkashin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, tare da cikakken goyon baya ga Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, suna kuma tabbatar da kudirinsu na kare zaman lafiya, hadin kai da ci gaban jam’iyyar a dukkan matakai

You must be logged in to post a comment Login