Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

An kori ‘yan wasan kasar Ingila biyu daga sansanin su

Published

on

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Ingila, Gareth Southgate, ya ce, an kori ‘yan wasa Phil Foden da Mason Greenwood daga masaukin ‘yan wasa, bisa zargin karya dokar killace kai a kasar Iceland.

Hukumar kwallon kafar ta kasar Ingla ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike kan batun.

Ingila ta yi nasara a wasan da ta buga a ranar Asabar da ci 1 da nema a filin wasa na Reykjavik.

Phil Foden, mai shekaru 20, dan wasan tsakiya ne a Manchester City, yayin da Mason Greenwood, mai shekaru 18, dan wasan gaba ne a Manchester United.

‘Yan wasa biyu na bugawa kasar ta Ingila yanzu haka sun koma gida domin ci gaba da killace kan su.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!