Connect with us

Labarai

An kwaso ‘yan Najeriya 145 da suka maƙale a Aljeriya

Published

on

Hukumar bayar d aagajin gaggawa ta kasa Nema ta karɓi ‘yan Najeriya 145 da aka kwashe zuwa gida bayan sun maƙale a Aljeriya ranar Litinin.

Hukumar National Emergency Management Agency ta ce mutanen sun sauka a filin jirgin sama na Legas da misalin ƙarfe 12:15 na rana a jirgin Air Algeria.

Nema ta ce ƙungiyar kula da ‘yan cirani ta International Organization for Migration (IOM) ce ta ɗauki nauyin kwaso mutanen bisa haɗin gwiwa da gwamnatin Najeriya.

Mutanen sun haɗa da maza manya 132, da yara tara, da jarirai huɗu.

A ranar Alhamis da ta gabata ma aka kwaso wasu ‘yan Najeriya 148 zuwa gida bayan sun maƙale a Sudan, a cewar Nema.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!