Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

‘Yan Najeriya sun kamo hanyar dawowa gida daga kasashen Malaysia da Thailand

Published

on

Hukumar kula da ‘yan Najeriya mazauna kasashen ketare ta ce a yanzu haka wasu ‘yan Najeriya da suka makale a kasashen Malaysia da Thailand sakamakon cutar Corona na kan hanyar su ta dawowa gida.

Hukumar ta bayyana hakan ne ta shafin ta na Twitter tana mai cewa mutanen sun taso ne daga filin jirgin saman Malaysia dana Kaula Lampour dake kasar Thailand cikin jirgin saman Air Peace inda kuma zasu sauka a biranen Abuja da Lagos a yau.

Sanarwar da hukumar ta wallafa, ta ce wannan shine karo na farko da aka fara kwaso ‘yan asalin kasar nan daga wadannan kasashe biyu, tun bayan da aka fara annobar Covid-19.

Mutanen sun baro kasashen biyu ne da misalign karfe 7 na safiyar yau, kuma anan sanya rana zasu sauka a filayen jiragen saman Nnamdi Azikiwe da ke birnin tarayya Abuja da kuma Murtala Muhammad da ke jihar Lagos.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!