Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamna ya naɗa wanda zai ci gaba da kula da ofishin sakataren Gwamnati

Published

on

Gwamna Abba Kabir Yusuf Ya Nada Shugaban Ma’aikata a matsayin wanda zai ci gaba da kulawa da ofishin sakataren Gwamnatin Kano Dakta Abdullahi Baffa Bichi Har Zuwa Lokacin Da zai Dawo Daga jinya a ƙasa mai tsarki ta Saudiyya.

Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya umurci shugaban ma’aikatan Alhaji Abdullahi Musa da ya kula da ofishin sakataren gwamnatin jihar Kano.

Hakan na kunshe ne ta cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar jiya laraba 06 ga Nuwamba 2023

Nadin ya biyo bayan hutun jinya da sakataren gwamnatin Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya yi wanda ya tashi daga kasar nan don jinya a kasar Saudiyya.

A wata takarda mai dauke da sa hannun shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano.

Shehu Wada Sagagi, Shugaban Ma’aikata zai ba da aikin kulawa har sai an dawo da sakataren gwamnatin a cikin ‘yan makonni masu zuwa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!