Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Gwamnatin Kano ta mika wa Abba Gida-gida kundin muhimman bayanai

Published

on

Shugaban kwamitin mika mulki na Gwamnatin Kano kuma sakataren gwamnatin Alhaji Usman Alhaji ya mika kundin da ke dauke da muhimman bayanai ga kwamitin karbar mulki da Dakta Abdullahi Baffa Bichi na jam’iyyar NNPP mai jiran rantsuwar kama aiki ke jagoranta karkashin jagorancin sabon zababben gwamna Injiniya Abba Kabir Yusif.

Da yake mika kundin ranar Larabar makon nan a gidan gwamnatin Kano a madadin gwamnan Dakta Abdullahi Umar Ganduje, Alhaji Usaman Alhaji, ya yaba da kokarin kwamitin karbar mulkin bisa hadin kai wajen gudanar da tattara bayanan da ya kamata.

Alhaji Usman Alhaji, a bayanin sa cikin harshen Turanci, ya yi fatan gwamnati mai shigowa za ta ci gaba da dorawa daga inda suka tsaya a fannin bunkasa jihar Kano da sauran fannonin ci gaban rayuwar mazauna jihar.

Da yake nasa jawabin, Shugaban kwamitin shirye-shiryen karbar milkin na jamiyyar NNPP Dakta  Abdullahi Baffa Bichi, ya ce, ya karbi kundin bayanan gwamnatin, kuma za su mika wa gwamna mai jiran gado Injiniya Abba Kabir yusif, domin ya yi masa duba na tsanaki musamman bayanan da ke kunshe a cikinsa.

Dakta Abdullahi Baffa Bichi ya kuma ce, shigowar gwnanatinsu zai kawo ci gaba da walwalar alummar jihar Kano.

 

Rahoton: Abba Isah Muhammad

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!